Jami’an ruwan na Italiya sun kuma yi nasarar kubutar da wani kwale kwale mai dauke da mutane 73, wadanda aka bayyana ‘yan Syria ne da Kurdawa da ‘Yan Somalia da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai.
Akalla mutane 480 aka tabbatar da mutuwarsu cikin watanni uku a bana wadanda ke kokarin shiga Turai.
A shekarar da ta gabata baki 3,500 daga Afirka da Gabas ta Tsakiya suka mutu a kokarin tsallakawa zuwa Turai.ABNA